Sojojin Yahudawan Sun Sake Aiwatar Da Kisan Kiyashi A Yankin Zirin Gaza

Sojojin yahudawan sahayoniyya sun gudanar da wani sabon kisan kiyashi a yankin Gaza ta hanyar kaddamar da hare-haren wuce gona da iri Rahotonni sun bayyana

Sojojin yahudawan sahayoniyya sun gudanar da wani sabon kisan kiyashi a yankin Gaza ta hanyar kaddamar da hare-haren wuce gona da iri

Rahotonni sun bayyana cewa: Fararen hula da dama da suka hada da kananan yara ne suka yi shahada tare da jikkata wani adadi mai yawa na Falasdinawa a sabbin hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan arewacin Zirin Gaza. Wadanda kisan kiyashin ya shafa kai tsaye sun hada da ‘yan gudun hijira da suka rasa muhallansu da kuma wadanda luguden bama-bamai suka tilasta musu tserewa daga gidajensu da kuma wadanda suke rayuwa a makarantu da asibitoci.

Yakin kisan kiyashi da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suke ci gaba da yi da nufin murkushe Falasdinawa a Zirin Gaza tun daga shiyar arewa zuwa kudu da tsakiyar yankin yana ci gaba.

A cewar majiyoyin kiwon lafiya na Falasdinu, adadin wadanda suka yi shahada a hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a yankuna Zirin Gaza tun daga wayewar garin jiya Litinin ya haura shahidai sama da 40, baya ga wasu da dama da suka samu raunuka, yayin da sojojin mamaya ke ci gaba da korar dubun dubatar Falasdinawa daga gidajensu da kuma hana su kayayyakin agaji musamman abinci, ruwa da magunguna isa gare su har tsawon kwanaki 17.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments