Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Jaddada Cewa Ba Su Jin Tsoron Makiya

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Ba su  tsoron abokan gaba, kuma za su mayar da martani mai tsanani kan duk wani

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Ba su  tsoron abokan gaba, kuma za su mayar da martani mai tsanani kan duk wani harin wuce gona da iri kan kasarsu

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf, ya bayyana matsayin Iran dangane da yakin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta kunna a Gaza da Lebanon.

Muhammad Baqir Qalibaf, ya yi tsokaci game da yadda ake ta yada hotonsa yana tuka jirgin sama da ya nufi kasar Lebanon, yana mai cewa: Kwarai ya sanar da cewa ya tuka jirgin sama zuwa kasar Lebanon, kuma tabbas suna son bayyana cewa ne suna koyi ne da jagoransu madaukaki, wanda ya jagoranci sallar Juma’a, duk da barazanar da makiya suke yi, ta hanya mafi kyawu, tare da halartar dimbin al’ummarsu masu girma wadanda a kodayaushe suke a fage.

Ya kara da cewa, a zahiri, shi da kansa ya tuka jirgin sama, kuma abin farin ciki ne ya kasance a tsakanin ‘yan’uwansu na Lebanon, da kuma cikin al’ummar Lebanon, don ziyarar wuraren da aka kai harin wuce gona da iri da wuraren da abin ya shafa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments