Haramtacciyar Kasar Isra’ila Na Kara Tsananta Hare-Hare A Gaza

Rahotanni daga yankin zirin Gaza sun tabbatar da cewa, Isra’ila ta kashe aƙalla mutum 16 tare da raunata wasu a harin da ta kai ta

Rahotanni daga yankin zirin Gaza sun tabbatar da cewa, Isra’ila ta kashe aƙalla mutum 16 tare da raunata wasu a harin da ta kai ta sama a kusa da Asibitin Al-Saeed Yaman da ke arewacin Gaza da aka yi wa ƙawanya.

Hossam Abu Safiya daraktan asibitin Kamala Adwan da ke Gaza ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Anadolu cewa an kashe mutanen ne a lokacin da wani jirgin yakin Isra’ila ya kai hari kan tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a wajen asibitin.

Jami’an agajin sun ce wadanda suka mutu sun hada da mata da kananan yara, inda suka ƙara da cewa harin bam din ya dagargaza “gawarwakin Falasdinawan da suka mutu.”

Bayan haka, an kashe Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu a wani hari na biyu ta sama da aka kai kan mutanen da suka rasa matsugunansu a wajen kofar asibitin, kamar yadda hukumar kare fararen hula ta Gaza ta sanar.

Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya ce Gaza da aka yi wa kawanya ta kasance “ba za a iya gane ta ba”, kuma babu alamar kawo ƙarshen tashe-tashen hankulan Isra’ila da suka mamaye yankin Gabas ta Tsakiya.

Philippe Lazzarini ya bayyana haka a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan halin da Falasdinawa ke ciki, inda ya ce, shekara daya bayan kazamin yakin Gaza, babu ranar kawo ƙarshen tashe-tashen hankulan da suka dabaibaye yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments