Dyniyarmu A Yau: Kan Hare Haren Wa’adus Sadik II

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku al-amura wadanda

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku al-amura wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro da sauran a duniya a cikin makon da ya gabata sannan mu yi masu karin bayani sai kuma daga karshe mu ji ra’ayin masana danagne da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da kuma a cikin shirimmu na yau.

A daren tarlatan da ta gabata ce 01ga watan Octoban shekara ta 2024 dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran (IRGC) suka maida martani kan HKI saboda laifuffukan da ta aikatawa kasar a cikin watanni da suka gabata da kuma kashe Sayyid Shahid Hassan nasarallah babban sakataren kungiyar Hizbullah. Kafin hakan itace ta kashe Shiekh Isma’il Haniyya shugaban kungiyar Hamas.

Sheikh Isma’il Haniyya dai ya zo kasar Iran a kuma birnin Tehran ne don hallatar bikin rantsarda sabon shugaban kasar Iran Masoud Paezeskiyan. Sai ma’aikatan HKI a nan Tehran suka kashe shi a masaukinsa da ke nan Tehran. Sun kashe tare da shi har da mai gadinsa

Gwamnatin kasar Iran a lokacin ta tabbatar da cewa zata  rama, amma bata bayyana lokaci da kuma ta yadda zata rama ba. Wannan karan kansa ya zama azaba ga HKI kanta da kuma kawayenya.  

Sai kuma a ranar jumma’a 27 ga watan satumban shekara ta 2024 jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan wasu dogayen gine gine guda 6 a unguwar Dahiya Junubiyya, ko kudancin birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon, bayan sun sami labaran liken asiri na samuwar sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Shahid Hassan Nasarallah a cikin daya daga cikin gine ginen. Inda jiragen nan suka sauke ton 80 na makamai masu linzami kan wadannan gine gine suka daidaita su da kasa.

Da haka kuma suka kashe Sayyid Hassan Nasarallah, ko sun kaishi ga shahada, da wasu yayan kungiyar wadanda suke tare da shi da kuma Manja Janar Abbas Nilfuroshan wani babban jami’in na dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran. Wanda kuma yake kula da al-amuran kungiyar ta Hizbullah a cikin dakarun na IRGC.

Bayan haka JMI ta ga cewa HKI ta cancanci ladabtarwa saboda laifufukan da ta aikata. Daga ciki dai sun kashe shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya a birnin Tehran ba a birnin Doha na kasar Qatar ba inda yake zaune.

Idan mun zurfafa tunani don abinda yasa gwamnatin HKI ta kashe, Isma’ila Haniyya a Tehran ba a Doha ba, zamu fahinci cewa tana son janyo JMI ta shiga yakin da HKI take fafatawa a Gaza ne, don tallafawa HKI ta kira sauran kasashen duniya, musamman kasashen yamma su taimaka mata a yakin da take fafatawa da Falasdinawa a Gaza, da Hizbullah a Lebanon da kuma kasar Yemen da Iraki.  

A cikin wannan halin ne a daren Talatan da ta gabata, wato 01 ga watan Octoban shekara ta 2024, dakarun IRGC tare da jagorancin kwamandan dakarun Janar Hussain Salami suka cilla makamai masu linzami samfurin Balistic da kuma wadanada ake kira Hipasonic kimani 400 zuwa kan cibiyoyin tsaro da barikokin sojoji na HKI inda – kamar yadda bayanan dakarun suka tabbatar- kashi 90% na makaman suka kai ga bararsu kamar yadda aka tsara a cikin HKI. Banda haka makaman sun yi barna da ake bukatar su yi ga sojojin gwamnatin yahudawan yar mamaya.

Bayan fara cilla makaman, dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran, shn fidda sun fidda bayani na farko dangane da hare hare. Banda haka wani mai magana a madadin sojojin HKI sun tabbatar da cewa JMI ta cilla makamai masu linzami suna kuma kan hanyarsu ta isowa haramtacciyar kasar.  

Wasu kafafen yada labarai na yanar gizo a cikin Iran sun dauki hotunan makaman a lokacinda suke kan hanyarsu ta zuwa HKI ta kan iyakar kasar da kasar Iraki. Banda haka sun ga lokacinda makamai masu linzami kimani 400 suke tashi daga wurare daban daban a cikin kasar.

Banda haka mutane da dama a cikin kasar Iran da kuma kasashen da makaman suka ratsa ta kansu duk sun dauki hotunan makaman, har da na bidiyo suna da Aikawa cikin yanar gizo kowa na gani.

Banda haka a lokacinda makaman suka fara fadawa kan cibiyoyin tsaro na HKI yahudawan sun yi ta daukar hotunansu suna Aikawa suma zuwa cikin yanar gizo.

A bisa wasu rahotannin daga HKI makaman na dakarun IRGC sun kan garuruwa da birani 13 daga cikin har da birnin Telaviv baban birnin haramtacciyar kasar da Haifa cibiyar kasuwanci da kuma babbatar tashar jiragen ruwa na kasar.

Har’ila yau kafafen yada labarai na HKI sun bada labarin tashin dukkan jiniyoyi gargadi a duk fadin kasar ta Falasdinu da aka mamaye. Sun kuma bukaci mutane su yi sauri su shiga wuraren da aka tanadar masu don kare kansu daga makaman makiya.

A cikin bayanan da dakarun juyin juya halin musulunci IRGC suka fitar bayan kammala hare haren sun ce, wadannan hare hare sun zo ne saboda daukar fansar Kishan shahida Isma’ila Haniyya shugaan kungiyar Hamas wacce take gwagwarmaya da HKI tun kimani shekara guda da ta gabata. Da kuma kissan shahidai Sayyid Hassan Nasarallah shugaban kungiyar Hizbullah na kasar Lebanon da kuma Manjo Janar Abbas Nilfurushan na dakarun IRGC da wadanda suke tare da su.

Har’ila yau dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar sun kara da cewa, idan HKI ta kuskura ta maida martani kan wadan nan hare hare, to lalle zata gamu da wasu sabbin hare hare masu tsanani fiye da na “Wa’adus Sadik II.

Sanarwan ta kara da cewa: An kai wadannan hare hare ne tare da amincewar majalisar koli ta tsaron kasa na Iran da kuma ma’aikatar tsaron kasar.

A wani labarin kuma mai magana da yawun sojojin HKI ya bukaci dukkan yahudawan su ci gaba da kasancewa cikin wurare masu kariya daga makamai wadanda aka tanadar masu har zuwa lokacinda aka tabbatar da amincin babu wani hatsari da ya rage.

Jaridar ‘Ma’arif ta yahudawa ta bada labarin cewa a cikin mintoci 30 ne kadai dukkan makamai masu linzami kimani 400 wadanda aka cilla daga kasar Iran suka iso HK kuma aka da zaran sun shiga kasar aka fara jin karar fashewa a ko ina.

Sai kuma Jaridar NewYork Time ta kasar Amurka, wacce ta bayyana cewa: Da alamun wasu daga cikin makaman sun isa HKI ne a cikin mintoci wadanda basu kai 15 ba saboda saurinsu, wanda hakan ya nuna cewa makaman samfurin bailistic ne masu sauri, ko wadanda ake kira supersonic.

Kafin isowar makaman dai gwamnatin HKI ta bada sanarwan rufe sararin samaniyar kasar ga jiragen sama masu isowa daga kasashen waje ko wadanda zasu tashi. Banda haka,  sannan jiragen sama ma su zaman kansu da suke tafiya a cikin kasar su yi sauri su sauka a tashoshin jirage mafi kusa da su.

New York Times ta ce dukkan jiniyoyin gargadi kimani 1,864 da aka kakkafasu a duk fadin kasar sun fara kara a dai dai lokacinda makaman suka shigo sararin samaniyar HK.

Har’ila yau kafafen yada labarai na HKI sun bayyana cewa mafi yawan makaman sun fada ne kan  cibiyoyin sojoji da kuma na tsaron kasar. Sannan Ben Gafir ministan tsaron cikin gida na HKI ya bukaci yansandan kasar su aika jami’an tsaro masu sa kai kai har 13,000 zuwa cibiyoyin ko ta kwana a duk fadin kasar.

A wani wuri jiridar ma’arif ta ce dakarun kare  juyin juya halin musulunci na kasar Iran IRGC sun cilla makamai fiye da 400 a cikin mintoci bas u fi 30 ba.

Sannan tashar talabijin ta HKI ‘Channel 12″ ta bada labari daga bakin wani jami’in gwamnatin kasar Amurka wanda baya son a bayyana sunansa,  ya na cewa gwamnatin Amurka ta taimaka wajen kakkabo wasu daga cikin makamai masu linzami wadanda JMI ta cilla kan cibiyoyin tsaro da sojoji na HKI.

Jaridar Ha’arith ta HKI ta nakalto mai aiko mata rahotanni Yusi Milmon ya na cewa, a dai dai lokacinda IRGC suka fara cilla  makamai masu linzami kan HKI, JMI ta kai hare hare ta yanar gizo kan kamfotoshin HKI don hana wasu garkuwan makamai masu linzami masu aiki da kumfutoci aiki.

Sannan dan rahotin ya riya cewa, wai Iran da aikawa wayoyin hannun yahudawan Sahyoniyya sakonni na karya, dauke da sakon cewa ‘an gama kai hare haren su fito daga inda suke boye’ alhali ta na ci gaba da kai hare hare.

Sai kuma tsohon shugaban kasar Amurka Donal Trump bayan ji labari kuma ya gani hare haren na kasar Iran kan HKI, ya rubuta a shafinsa na X kan cewa, ‘ana iya kaucewa wannan yakin, sannan ya ce, da shi ne shugaban kasar Amurka da  ba’a yi wannan yakin ba.

Tashar talabijin ta ABC ta kasar Amurka ta ita ma ta nakalto wani jami’in gwamnatin Amurka na cewa Amurka ta taimaka wajen kakkabo wasu daga cikin malamai masu linzami wadanda iraniyawa suka cilla kan HKI.

Sannan daga karshe tashar Talabijin ta ‘Channel 13’ ta HKI ta bayyana cewa Firai ministan kasar Benyamin Natanyahu ya na tare da wasu ministocinsa a wani wuri a karkashin kasa a lokacinda makamai masu linzami na kasar Iran suka fara faduwa a cikin kasar.

Kungiyoyin Falasdinawa da dama, wadanda suka hada da Hamas, Jihadul Islami, Jibhatush Sha’abia na Falasdinawa duk sun yaba da hare haren na kasar Iran kan HKI.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments