Hotunan Tauraron Dan’adam Sun Nuna Barnar Da Makaman Iran Su Ka Yi Wa HKI

Hotunan tauraron dan’adam da kamfanin dillancin labarun “Associated-Press” ya buga sun nuna girman barnar da ya shafi filin sauka da tashin jiragen sama mafi gima

Hotunan tauraron dan’adam da kamfanin dillancin labarun “Associated-Press” ya buga sun nuna girman barnar da ya shafi filin sauka da tashin jiragen sama mafi gima da muhimmanci a Isra’ila sanadiyyar makamai masu linzami da Iran ta harba.

Ita ma tashar telabijin din CNN ta Amurka ta bayyana cewa, makamai masu yawa da Iran din ta harba sun sauka akan cibiyar ta Nifatim” da take a cikin saharar Naqab, kuma wasu makamai sun yi barna a cibiyar      “ Tel Nov, mai nisan kilo mita 15 daga kudancin Tel Aviv.

Hotunan na tauroron dan’adam sun nuna yadda  fasa saman garejin da ake ajiye jiragen yaki samfurin F-15 da HKI ta yi amfani da su wajen jefa bama-baman da su ka yi sanadiyyar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah.

A wani rahoto da tashar talabijin din “Cane” ta HKI ta watsa ta bayyana cewa; Da akwai gidaje 101 da hare-haren na Iraniyawa su ka lalata a cikin yanki daya na Hod Shaharun.

Bugu da kari wasu daga cikin makamai masu linzamin da Iran ta harba sun sauka a kusa da cibiyar kungiyar leken asirin Isra’ila ta Mosad a kusa da birnin Tel Aviv.

Jim kadan bayan kai harin, kafafen watsa labarun HKI da jami’an Amurka sun yi kokarin nuna cewa, babu wani tasiri da harin na Iran ya yi. Yanzu da bayanai su ka fara fitowa suna tabbatar da akasin hakan.

Jaridar “Ma’ariv” ta HKI ta ambaci cewa, barnar da makaman na Iran su ka yi, za su sanya alamar tambaya akan makaman tsaron HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments