Ministan Harkokin Wajen Iran: Kashe Jami’in Iran A Lokacin Kai Hari Kan Sayyid Nasrallah Zai Fuskanci Mayar Da Martani 

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kisan gillar da                 aka yi wa Birgediya Janar Nilforshan ba zai shige ba tare da martani ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Kisan gillar da                 aka yi wa Birgediya Janar Nilforshan ba zai shige ba tare da martani ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Babu ko shakka wannan danyen aikin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata ba zai taba shigewa ba tare da fuskantar mayar da martani ba, kuma Iran za ta yi amfani da dukkanin karfinta na siyasa, diflomasiyya, shari’a da kasa da kasa wajen mayar da martani mai gauni kan masu aikata laifuka da masu goyon bayansu.

A cikin ta’aziyyarsa ga kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Manjo Janar Hossein Salami, ministan harkokin wajen kasar Iran ya dauki wannan aiki a matsayin babban laifi na matsorata kuma dalili a fili kan irin ta’addanci da muggan laifukan yahudawan sahayoniyya da kuma magoya bayansu.

Har ila yau A cikin sakon ta’aziyyarsa kan shahadan babban kwamanda kuma daya daga jagororin tsoffin mayaka da wadanda suka samu raunuka a yakin kare kai mai alfarma na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran mujahid Birgediya Janar Abbas Nilforshan da ya yi shahada a lokacin da aka kai hari kan Sayyid Hasan Nasrallah babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ga jagoran juyin juya halin Mususlunci na Iran da iyalan shahidin mai girma da daraja da abokai madaukaka da al’ummar Iran masu girma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments