Amurka: Sauyi Na Gaske Tana Kan Tituna Ne Ba A Akwatin Zabe Ba

Sauyi na gaskiya a kan titunan biranen Amurka yake ba a akwatin zabe ba. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa ba

Sauyi na gaskiya a kan titunan biranen Amurka yake ba a akwatin zabe ba. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa ba bambanci tsakanin jam’iyyun siyasa guda 2 a Amurka idan al-amarin ya shafi kissan kiyashin da gwamnatin kasar tare da HKI suke yi a Gaza ne.

Labarin ya kara da cewa yan siyasa a kasar Amurka basu damu da kururuwan dubban daliban Jami’o’in kasar suke yi tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata ba. Kururuwa na bukatar gwamnatin kasar ta dakatar da aikawa HKI makamai wadanda take kissan falasdinawa da su.

A yakin neman zaben Donal Trump dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Repuclican da kuma Kamala Haris na jam’iyyar Democrate, gaba daya babu batun dakatar da aika makamai zuwa HKI wanda daliban jami’mi’o’in kasar suke kururuwa a yi hakan tun kimani shekara guda da ta gabata.

A cikin daya daga cikin tarurrukan yakin nemen zaben shugaban kasan Amurka wanda Kamal Haris mataimakin shugaban kasa kuma yar takarara neman shugaban kasa a karkashin tutar Jam’iyyar Democrates tayi, wasu sun ce mata ‘ana tuhumar ki da kissan kare dangi a gaaza’ da ta ji haka ta ce: Idan kuna son Trump ya sake dawowa kan kujerar shugabancin kasar Amurka ku ci gaba da wannan zargin.

Sannan an nakalto Trump , shi ma a wani taron yakin neman zabe, yana cewa ‘idan ya sake hawa kan kujerar shugabancin kasar Amurka to kuwa zai ce wa Natanyahu ya zo ya karasa aikin da ya fara a gaza na kissan Falasdinawa.  A halin yanzu dai ya rage kwanaki a gudanar da zaben shugaban kasa a Amurka, daliban jami’o’i a Amurka wadanda suke nuna damawarsu da kissan kare dangi wanda gwamnatin kasar tare da HKI suke yi a  gaza suna cikin dimwa dangane da zaben.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments