Jamus, Faransa Da Birtaniya Sun Kakaba Wa Iran Takunkumi Kan Zargin Mikawa Rasha Makamai

Kasashen Jamus da Faransa da Birtaniya sun kakaba wa Iran sabbin takunkumai, bisa zarginta da mika wa Rasha makamai masu linzami da za ta yi

Kasashen Jamus da Faransa da Birtaniya sun kakaba wa Iran sabbin takunkumai, bisa zarginta da mika wa Rasha makamai masu linzami da za ta yi amfani da su a yakin Ukraine, zargin da Tehran ta yi watsi da shi.

Kasashen ukun sun ce, sun tabbatar da cewa Iran din ta aikawa makamman.

Sanarwar ta bayyana mika makaman a matsayin wani ci gaba na goyon bayan sojojin Iran ga kasar Rasha, lamarin da ke zama barazana kai tsaye ga tsaron kasashen Turai tare da yuwuwar makamai masu linzami na Iran su isa kasashen Turai.

Kasashen ukun sun ce sun dauki matakin gaggawa na soke yarjejeniyoyin jiragen sama tsakaninsu da Iran.

Har ila yau, suna shirin ayyana wasu matakai kan hukumomi da daidaikun mutane da ke da hannu a shirin makami mai linzami na Iran da kuma mika makamai masu linzami da sauran makamai zuwa kasar Rasha.

Bugu da kari, za su yi kokarin kakaba takunkumi kan jiragen saman Iran, kamar irin yadda  Washington ta yi.

Sanarwar ta zo ne duk da watsin da Iran ta yi da zargin na aikewa da makamai zuwa Rasha domin amfani da su a Ukraine.

Gabanin sanarwar ta hadin gwiwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanani ya fada a shafin X cewa ” yada labaran karya da mika makaman Iran ga wasu kasashe” farfaganda ce” kuma karya ce.

Shi ma sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba Amurka za ta kakabawa Iran sabbin takunkumai.

A wata ziyara da ya kai birnin Landan, ya yi ikirarin cewa Iran ta aike da makamai masu linzami masu cin gajeren zango zuwa Rasha, wadanda ake sa ran za a yi amfani da su kan Ukraine cikin makonni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments