HKI Tana Fuskantar Matsalolin Tattalin Arziki Da Kudade Masu Tsanani Saboda Yakin Gaza

Jaridar Damorkor ta HKI ta bayyana cewa kasar zata shiga matsalolin tattalin arziki da kudade saboda yakin da ke faruwa a Gaza da kuma da

Jaridar Damorkor ta HKI ta bayyana cewa kasar zata shiga matsalolin tattalin arziki da kudade saboda yakin da ke faruwa a Gaza da kuma da tsaron hare haren da kawayen Falasdinawa suke kaiwa kanka.

Kamfanin dillancin labaran Sahab na JMI ya bayyana cewa, al-amuran tsaro sun tabarbare a HKI sosai ba kamar yadda ake zato ba. Jaridar ta kara da cewa gwamnatin Benyamin Natanyahu ta fuskanci matsaloli da dama a kasafin kudin na shekara ta 2023-2024, sannan zata fuskanci matsaloli a cikin kasafin kudi na shekara mai zuwa ta 2025, wadanda hakan zai kara lalata tattalin arzikin kasar.

Tattalin arzikin HKI tana fuskantar matsaloli da dama tun bayan fara yakin Tufanul Aksa, kuma kudaden shiga sun ragu sosai ta yadda gwamnatin HKI ta ajiye wasu ayyukan ci gaba kuma wannan halin zai kara munana a cikin yan watanni masu zuwa inji Jaridar.

Banda haka batun zuba jari a kasar ya zama tarihi a halin da muke ciki, banda kudaden masu yawa wadanda gwamnatin kasar ta rika zubawa a yakin Gaza, ga kuma yadda kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta kori mafi yawan mutane a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye, wanda ya rage kudaden shiga masu yawa da gwamnatin kasar ta ke samu.

Duk tare da tallafin da babu iyaka, wanda HKI take samu daga kasar Amurka da kuma sauran kasashen yamma ba za ta tsira daga lalacewar tattalin arzikin kasar ba, inji jaridar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments