Indonesiya da Koriya ta Kudu na shirin yin watsi da dala a harkokinsu na kasuwanci

Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya bayar da rahoton cewa, Indonesia da Koriya ta Kudu sun amince da wani tsarin hadin gwiwa na aiwatar da hada-hadar

Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya bayar da rahoton cewa, Indonesia da Koriya ta Kudu sun amince da wani tsarin hadin gwiwa na aiwatar da hada-hadar kudin gida (LCT) tsakanin kasashen biyu da nufin inganta amfani da kudin Rupiah na Indonesia da kuma na Koriya ta Kudu, a cinikayyar kasashen biyu.

A cikin wani rahoto da Jakarta Globe ta ruwaito, kamfanin dillancin labaran Barna ya sanar da cewa an kammala yarjejeniyar ne a karshen wannan mako.

A cewar rahoton, babban bankin kasar Indonesia (BI) na neman rage dogaro da dalar Amurka ta hanyar kulla alaka mai inganci da bankin Koriya ta Kudu (BOK).

An tsara tsarin LCT tsakanin Indonesia da Koriya ta Kudu zai fara aiki a ranar 30 ga Satumba.

A cikin wata sanarwa da shugaban sashen sadarwa na babban bankin kasar Indonesiya Erwin Haryono ya fitar, ya ce: Aiwatar da tsarin LCT tsakanin Indonesia da Koriya ta Kudu wani ci gaba ne na hadin gwiwar hada-hadar kudi tsakanin kasashen biyu.

Dangane da haka, Irwin ya ce: Ana sa ran aiwatar da tsarin LCT tsakanin kasashen biyu zai kara karfafa mu’amalar cinikayya tsakanin kasashen biyu, da rage hadarin musayar kudaden waje, da kuma inganta yadda ake gudanar da hada-hadar kudi.

BI da BOK sun sanya bankuna da yawa a matsayin bankunan ACCD a Indonesia da Koriya ta Kudu don tallafawa aikin tsarin Rupiah-Won LCT.

Tare da wannan yarjejeniya, yanzu babban bankin Indonesia ya kafa tsarin LCT tare da wasu ƙasashe da yawa, ciki har da Indiya, Malaysia, Thailand, Japan, China da Singapore.

Indonesiya tare da kasashe da dama na duniya sun dade suna daukar matakan rage dogaro da dala a harkokin kasuwanci, bil hasali ma manufofin Amurka na matsin lamba kan kasashen da ba sa bin manufofin Washington, tare da yin amfani da takunkumin tattalin arziki a  kansu domin karya da durkusar da tattalin arzikinsu, hakan ne ya sa wadannan kasashe ke amfani da kudaden kasa wajen hada-hadar kasuwanci tsakaninsu.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin,  a baya ya bayyana cewa Amurka ta bata sunan asusun ajiyar kudi na kasa da kasa ta hanyar amfani da dala a matsayin wani makami na cutar da tattalin arzikin kasashe masu sabanin siyasaa da ita.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments