An Yi Musayar Wuta A Karo Na Farko Tsakanin Indiya Da Pakistan A Yankin Kashmir Wani Jami’in tsaron kasar Pakisatn ya bayyana cewa a jiya

An Yi Musayar Wuta A Karo Na Farko Tsakanin Indiya Da Pakistan A Yankin Kashmir

Wani Jami’in tsaron kasar Pakisatn ya bayyana cewa a jiya da dare an yi musayar wuta na farko tsakanin sojojin kasashen Pakisatan da Indiya, tun bayan rikici ya sake dawowa a yankin Kashmir na kan iyakokin kasashen biyu.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto wani babban jami’in tsaron kasar ta Pakisatn Ashfaq Jilani yana cewa sojojin bangarorin biyu sun yi musayar wuta kan iyakokin kasashen biyu a Kashmir a jiya da dare.

Labarin har’ila yau ya nakalto kamfanin dillancin labaran France Press ya nakalto Jilani yana fadar haka a safiyar yau jumma’a, ya kuma kara da cewa babu wani rahoto dangane da musayar wautan da ya shafi fararen hula. Don haka al-amura na tafiya a cikin garuruwan da suke yankin ‘Wadi-Libo’.

Wannan na zuwa ne bayan wani hari da aka kai a yankin a cikin kwanakin da suka gabata wanda ya kai ga mutuwar jami’an yansandan kasar India 26.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments