Uganda Ta Kulla Yrjeniya Da Kamfanin UAE Don Hakar Gina Matatan Man Fetur A kasar Gwamnatin kasar Uganda ta bada sanarwan kulla yarjeniya da

 

Uganda Ta Kulla Yrjeniya Da Kamfanin UAE Don Hakar Gina Matatan Man Fetur A kasar

Gwamnatin kasar Uganda ta bada sanarwan kulla yarjeniya da kamfanin Alpha MBM na kasar Haddiyar daular Larabawa saboda gina matatar mai wacce zata tashe man fetur ganga 60,000 a ko wace rana a kasar.

Jaridar Sputnik na kasar Rasha ya bayyana cewa Alpha MBM na wani hamshakin dan kasuwa ne mai suna Sheikh Maktoum bin Mohammed bin Rashid dan gidan sarautar kasar wanda yake zuba hannu jari a kasashen Afirka.

Yarjeniya tsakanin bangarorin biyu ta bukaci Alpha MBM ya rike kasha 60% na jarin kamfanin a yayinda gwamnatin kasar Uganda zata rike sauran kasha 40.

Banda haka zasu shimfida bututan mai daban daban na tsawon kilomita 212. Har’ila yau da kuma gina rumbunan ajiyar makamashi wanda zai lakume dalar Amurka Billiyon $4.

Kasar Uganda dai ta dade tana neman masu zuba jari a don haka da kuma sarrafa danyen man fitur wanda aka kiyasta ya kai ganga billiyon 6.5.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments