Kungiyar Tarayyar Turai (EU) Ta Sanya Sabbin Takunkuman Tattalin Arziki Kan Kasar Rasha Kungiyar tarayyar Turai wato EU ta kakabawa kasar Rasha sabbin takunkuman tattalin

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) Ta Sanya Sabbin Takunkuman Tattalin Arziki Kan Kasar Rasha

Kungiyar tarayyar Turai wato EU ta kakabawa kasar Rasha sabbin takunkuman tattalin arziki a dai dai lokacinda yakin Ukraine yake cika shekaru 3 da faraway.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce kasashen kungiyar EU sun kakabawa kasar Rasha takunkuman tattalin arziki har 16 ne, wadanda suka hada da bangren tattalin arziki, kayakin yaki da masana’antu.

Labarin ya kara da cewa Kaja Kallas Jami’ar kungiyar mai kula da al-amuran kasashen waje da kuma harkokin tsaron kungiyar ce ta bayyana haka. Ta kuma kara da cewa sabban takunkuman suna saran zasu rage karfin kasar Rasha, su tilasta mata dakatar da mamayar da takewa kasar Ukraine. Kuma a dayan bangare ta bayyana cewa ta na kokarin kawo karshen yakin.

Kallas ta kara da cewa takubkuman EU a wannan karon za su hada har da jiragen ruwan masu daukar makamanshin kasar Rasha zuwa kasashen duniya, da kuma bankuna wadanda suke taimakawa harkokin saya da sayar da danyen man fetur na kasar ta Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments