Halvardeh ko Halva Shekari

Halvardeh ko Halva Shekari, na daya daga cikin alawoyin kasar Iran mai matukar amfani ga jikin dan adam, kuma anayin wannan alawan ne daga markadadden ridi. Halvardeh tana da dandano mai zaki kuma anfi ci da bredi a lokacin karin kumallo.

Gidan tsara mulki

Wannan gida na tsara tsaran mulki na birnin tabriz yana a wannan yanki mai suna azarbaijan wanda yake na gwamnati ne, wannan ginin tsawon shekaru da dama kusan daga shekarar ali dubu daya da dari tara da shida (1906) yazama wurin na shawar wari da duk wanda ke cikin wannan motsi, tarukan na gudana da tsarin mulki na wannan kasa wato Iran.

Godiya al'adar Iraniyawa

Jama'ar Iran na godiya da kyakkyawan kauyen Khaneqah wanda yake a yankin lardin Kermanshah, suna godiya ga Allah daya basu albarkar noman rumman.

​Kogin hoda (Pink lake) ya wuce Yanayi

Mun saba da ganin ruwa a shudi (blue) ko watakila kore-kore (greenish). A nan tafki ne da yazo da yanayi na daban na ruwan hoda. Tafkin Lipar Lake (wanda aka sani da ruwan hoda pink lake) ya samo asali saboda wani abu mai tsabta wanda ke dauke da daruruwan halittun ruwa na planktons a wannan yankin.

Magudanar Ruwa (Natural pesticide waterfall)

Magudanar Ruwa (Natural pesticide waterfall) Magudanar Ruwan Takht-e Soleyman, wanda aka sani da Ab-e Malakh (grasshopper’s water) yana daya daga cikin wurare masu ban-mamaki da aka sani sukai suna sosai a Isfahan, Iran. Ruwan da ke gudana daga Takht-e Soleyman ya ƙunshi wasu sinadirai da suke aiki a matsayin magungunan ƙwari a cikin gonakin yankin.

Lambun da Benen Rahim Abad

South Khorasan

Bene da Lambun Rahim Abad suna garin Birjand ne, kuma sun kasance daga cikin lambuna mafiya kyau a kasar Iran, kuma a kauyen da ake kira da Rahim Abad. Lambun Rahim Abad yana da mashiga guda biyu, kuma babu wata hanyar shiga cikin kwaryar lambun sai ta wadannan mashigar biyu. Bene da lambun Rahim Abad da ke garin Birjand yana da matsayi na musamman a tsakanin lambunan Iraaniyawa saboda irin tsarin gininsu da kuma adon da ranbada musu. Wannan babban ginin yana dauke ne da lambu, bene, wuraren ajiye kayayyaki, kududdufi, dakunan masu hidima, hasumiyar masu gadi da sauransu. Babban benen wannan lambu yana da hawa biyu. Hawa na kasa yana dauke da wuraren ajiya kayayyaki da kuma wurin gudanar da liyafa, sannan hawa na sama yana dauke da manyan dakunan taro da wasu karin dakuna na daban. Bangare na musamman a wannan bene shi ne babban dakin taron da aka kawata shi da madubi. An gina wannan benen ne a shekara ta 1351 Hijira Shamsiyya, bisa umurnin Isma’il Khan kuma ana amfani da wurin a matsayin fadar mulki. Cibiyar kula kayayyakin tarihi da al’adu ta sayi wannan babban bene a shekara ta 1380 daga Mu’assasar Mostazafan, sannan aka mayar da shi babbar cibiyar al’adu a shekara ta 1381. A yanzu haka ana amfani da wurin ne a matsayin wani bangare na gudanar ayyukan kyautata al’adu da kula da kayan tarihi da ayyukan hannu gami da yawon bude ido, sai dai a halin yanzu ba a gudanar da ayyukan al’adu da na yawon bude ido a wannan cibiya. An yi wa wannan wurin tarhi rajista ne a ranar 22 ga watan Khordad a shekara ta 1379 a matsayin wurin tarihi na kasa mai dauke da lamba 2707.

utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸ utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸ utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸utf-۸ utf-۸