Najeriya: Hukumar EFCC Ta Kama Mutane Fiye Da 65 Bisa Ga Aikata Laifukan zabe
2023-03-19 13:15:09

Hukumar yaki da yiwa tattalin arziki ta’annuti a tarayyar Najeriya EFCC ta bada sanarwan kama mutane fiye da 65 saboda tuhumar aikata laifuffukan da suka danganci zaben gwamnonin da aka gudanar a jiya Asabar a jihohi 28 a kasar.
Tashar talabijin ta “Channeltv” ta nakalto kakakin hukumar Wilson Uwujaren yana fadar haka ya kuma kara da cewa jami’an hukumar sun kama mutane 20 a yankin Ilorin na jihar Kwara, a yayinda wasu 13 kuma an kamasu a yankin Kaduna. Banda su an kama wasu da dama daga sauran jihohin da aka gudanar da zaben.
Har’ila hukumar ‘yansanda a Najeriya ma ta bada sanarwan kama mutane 12 a birnin Potakwal na jihar Rivers dangane da laifuffukan zabe, sai kuma guda 4 kuma a karamar hukumar Uyo na birnin Calabar.
Sauran wadanda aka kama sun fito ne daga jihohin Gombe, Sokoto, Kebbi da kuma Niger.
Sai dai duk da aka ana iya cewa an gudanar da zabubbukan gwamnoni da na yan majalisun jihohi cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!