​Raeisi: Burin Makiyan Iran Shi Ne Sanya Yanke Kauna A Zukatan Al’ummarta

2023-03-18 21:31:19
​Raeisi: Burin Makiyan Iran Shi Ne Sanya Yanke Kauna A Zukatan Al’ummarta

Shugaban kasar Iran Ibrahim Raeisi ya yaba da nasarorin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu da kuma yunkurin ci gaba na tsawon wadannan shekaru, yana mai cewa makiya na neman sanya yanke kauna a tsakanin al'umma da mayar da karfin kasar zuwa ga rauni.

Raeisi ya bayyana hakan ne a wani bikin kaddamar da wasu sabbin hanyoyin jiragen kasa na birane a Tehran babban birnin kasar ranar yau Asabar.

Raeisi ya ce "A yau, makiya suna neman sanya yanke kauna, rashin godiya da rashin taimako a cikin al'umma, amma mu al'ummar Iran mun yi imani da cewa duk abin da muka sanya a gaba za mu iya'."

A karkashin hadin gwiwar da ke tsakanin gwamnatin Iran da al'ummar kasar, shugaban ya ce an gudanar da ayyuka da dama a kasar, kana kuma ana ci gaba da gudanar da wasu manyan ayyukan, wadanda za a cimma su ta hanyar kokari da jajircewar matasan kasar.

"A yau, yanayin aiki da kokari ya mamaye kasa, kuma irin wannan yanayi ba shakka zai samar da gamsuwa da amincewar jama'a, da kuma karfafa gwiwar al’ummar kasa," in ji Raeisi.

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!