Tsohon Pira Ministan kasar Pakistan Imran Khan Zai Gurfana A Gaban Kotu

Lauya mai bayar da kariya ga tsohon pira ministan kasar ta Pakistan, ya fadawa manema labaru cewa a yau ne Imran Khan zai gurfana a gaban wata kotu a birnin Islamabad.
Lauyan
tsohon Pira ministan, Azhar Siddiqy ya kuma ce; Bayan da Imran Khan ya baro
babbar kotun koli dake Lahor, zai gurfana a gaban wata karamar kotu wacce take
a birnin Islamabad.
Kwanaki kadan
da su ka gabata ne dai wata kotun kasar ta Pakistan ta fitar da sammacin a kamo
tsohon Pira minista Imran Khan, da hakan ya sa aka aike da jami’an ‘yan sanda a
kusa da gidansa domin kama shi.
Sai dai
magoya bayansu sun yi taho mu gama da jami’an ‘yansandan, da hana a kama shi.
A halin da
ake ciki a yanzu dai kotun da aike da sammacin kamo tsohon Pira ministan ta
janye, da hakan ya sa aka sami mafitar da ta bai wa Imran khan zamar kai kansa
da kansa a gaban wata karamar kotu a birnin Islamabad.
Imran Khan
dai ya sha bayyana tsoronsa akan cewa mahukuntan kasar suna son kashe shi ne
idan sun kai shi gidan kurkuku, domin ba su son ya sake tsayawa takara a zabe
mai zuwa a watan Oktoba na wannan shekarar.
A ranar 9 ga
watan Aprilu na 2022 ne dai majalisar dokokin Pakistan ta tsige Pira minista
Imran Khan daga kan mukaminsa inda mambobinta 174 suka kada kuri’ar amincewa,
ba tare da an kada ko da kuri’a daya ta goyon bayansa ba.