Sabon Babi Tsakanin Saudiyya Da Turkiyya, Bayan Kisan Khashoggi

2022-06-23 09:37:20
Sabon Babi Tsakanin Saudiyya Da Turkiyya, Bayan Kisan Khashoggi

Kasashen Turkiyya Da Saudiyya, sun bayyana ziyarar da yerima mai jiran gado Mohamed Ben Salman ya kai a Ankara, a matsayin wani sabon babi a tsakaninsu.

Ziyarar dai ita irinta ta farko tun bayan kisan dan jaridan nan Jamel Khashoggi, a karamin ofishin jakadancin Saudiyya na Satambul, wanda ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Yayin ziyarar MBS, ya gana da shugaban Turkiyya Turkiyya Recep Tayyib Erdogan, inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi kasashen biyu, musamman kan tattalin arziki yawan bude ido da dai saurensu.

Jiya Laraba ne yarima mai jiran gado na Saudiyya, MBS, ya isa kasar Turkiyya a gajeren ran gadin da ya yi a yankin.

Saidai bangarori da dama a Turkiyya sun soki ziyarar ta MBS, dake zuwa shekaru uku bayan kisan dan jaridan da ake zargin Ben Salman din da hannu a ciki.

Kafin Turkiyya Mohamed Ben Salman, ya ziyarci kasashen Masar da Jordan.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!