Togo Da Gabon Zasu Zama Mamba A Kungiyar Kasashe Renon Ingila

2022-06-23 09:31:46
Togo Da Gabon Zasu Zama Mamba A Kungiyar Kasashe Renon Ingila

Taron kasashe renon Ingila ko Commonwealth, na bana zai amince da kasashen Togo da kuma Gabon a matsayin mamba, bayan shafe shekaru na bukatar hakan daga kasashen biyu na Afrika masu amfani da harshen faransanci.

A gobe Juma’a ne ake bude taron na kasashen Commonwealth, a birnin Kigali na kasar Rwanda.

Saidai shugabanin kasashen na Togo da Gabon ba zasu laraci taron na gobe ba, amma za’a gayyace su a hukumance bayan kasancewarsu mama a kungiyar a taron kungiyar nag aba.

Kungiyar kasashen renon Ingila dai ta kunshi mambobi 54 da suka hada da kasashe 19 daga nahiyar Afrika.

Masana na ganin farfadowar tattalin arzikin da Rwanda ta yi bayan zama mamba a kungiyar a 2009, shi ne ya ja hankalin kasashen shiga kungiyar.

Saidai kuma ana ganin hakan a matsayin wata alama ta Biritaniya ta karfafa hulda tun bayan data fice daga kungiyar tarayyar turai.

024

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!