​Yahudawa Sun Kai Samame A Cikin Masallacin Quds

2021-09-14 14:53:00
​Yahudawa Sun Kai Samame A Cikin Masallacin Quds

Wani adadi mai yawa na yahudawa 'yan share wuri zauna sun kutsa kai a yau Litinin a cikin masallacin aqsa.

Kafofin yada labarai na Falastinu sun bayar da rahoton cewa, wani adadi mai yawa na yahudawa 'yan share wuri zauna sun kutsa kai a yau Litinin a cikin masallacin aqsa tare da keta alfarmar wannan wuri mai daraja.

Yahudawan sun shiga cikin harabar masallacin ta hanyar kofar Magariba, daya daga cikin muhimman kofofin masallacin aqsa.

baya ga haka kuma jami'an tsaron gwamnatin a cikin kayan sarki dauke da bindigogi ne suke ba su kariya domin hana Falastinawa daukar wani mataki na hana yahudawan shiga cikin masallacin.

'Yan sahyuniya dai suna shiga wannan wuri ne da sunan suna kai ziyara a wani haikal da suke raya cewa na yahudawa ne da annabi Sulaiman ya ajiye a wurin.

Hakan kuma jami'an tsaron Isra'ila sun kame wasu Falastinawa 7 saboda nuna rashin amincewarsu da keta alfarmar wannan wuri mai daraja da yahudawan 'yan share wuri zauna suke yi.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!