​Rahoto: Mutane 480 Suka Rasa Rayukansu A Burkina Faso A Hare-Haren ‘Yan Ta’adda

2021-09-14 14:41:02
​Rahoto: Mutane 480 Suka Rasa Rayukansu A Burkina Faso A Hare-Haren ‘Yan Ta’adda

Kungiyar agaji ta kasar Norway tace ‘Yan bindigar da ke da’awar jihadi a Burkina Faso sun kashe mutane akalla 480 tsakanin watan Mayu zuwa Agustan wannan shekara.

Gidan Rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, kungiyar agajin ta bayyana damuwa dangane da karuwar yawan mutanen da ke mutuwa da kuma rasa matsugunan su a watannin da suka gabata.

Wannan na zuwa ne ganin yadda aka tilasta wa mutane sama da dubu 275 tserewa daga matsugunan su domin tsira da rayukansu tun daga watan Afrilun da ya gabata.

Alkaluman kungiyar sun nuna cewar akalla mutane dubu 55 ne ake rabawa da matsugunansu kowanne wata, abin da ke nuna yadda adadin ya ninka har sau 3 sabanin yadda aka gani tsakanin watan Oktobar shekarar da ta gabata zuwa watan Maris na shekarar da muke ciki.

Rahotan kungiyar ya ce alkaluman sun nuna cewar mutane sama da miliyan guda da dubu 400 ne suka tsere daga gidajensu domin kauce wa hare-haren.

Kungiyar ta ce tsaikon da ake samu wajen kaiwa jama’a dauki domin ba su kayan jinkai, hakan na tilastawa mutane zabi tsakanin matsalar tsaro da kuma yunwa.

Rahotan kungiyar ya ce wannan yasa wasu mutane suna zabin ci gaba da zama a yankunan da ‘Yan bindigar suka mamaye, duk da karancin abincin da suke fuskanta, abin da ke kaiga wasu cin ganyen itatuwa domin su ci gaba da zama a raye.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin Burkina Faso da ta bata izinin shiga yankunan domin taimakawa jama’ar dake fuskantar wannan matsala.

Daraktan kungiyar a Burkina Faso, Manenji Mangundu yace kungiyoyin agaji na da karfin taimakawa jama’ar dake cikin yankunan da zuwa gare su ke tattare da hadari.

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!