Iran: Jagora Yayi Afuwa Ko Rage Tsawon Dauri Ga Wasu Fursunoni Saboda Sallar Layya Da Idin Ghadir

2021-07-31 20:51:33
Iran: Jagora Yayi Afuwa Ko Rage Tsawon Dauri Ga Wasu Fursunoni Saboda Sallar Layya Da Idin Ghadir

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Imam Ayatullahi Sayyid Ali Khamenei ya amince da bukatar alkalin alkalan kasar na yafewa ko kuma rage tsawon hukuncin da aka yankewa wasu fursunoni a kasar, saboda zagayowar salla babba da kuma Idin Ghadir.

Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto jami’i mai kula da al’amuran watsa labarai na ofishin jagoran ya na fadar haka a yau Asabar.

Kafin haka dai Alkalin alkalan kasar Iran Gholam-Hossein Mohseni-Ejei ya rubutawa Imam Khamenei wasika inda a cikinta, ya bukaci jagoran ya yi rangwame ko ya yafewa fursunoni 2,825 hukuncin da aka yanken masu a kutuna daban-daban na kasar saboda zagayowar wadannan kwanaki farinciki masu alfarma.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!