Kasashen Afirka 14 Sun Kudurin Aniyar Korar Isra’ila Daga Tarayyar Afirka

2021-07-31 20:32:25
Kasashen Afirka 14 Sun Kudurin Aniyar Korar Isra’ila Daga Tarayyar Afirka

Bayan da haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ta ba da sanarwar shiga cikin kungiyar tarayyar Afirka (AU) a cikin yan kwanakin da suka gabata, kasar Aljeriya tare da wasu kasashen Afirka 13 sun kuduri anniyar korarta daga tarayyar.

Shafin yanar gizo na labarai, mai suna Rayul-Yaum ya nakalto wata tashar talabijin ta kasar Aljeria tana fadar haka ta kuma kara da cewa, ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Ramadan Lama’amra ya na cewa kungiyar tarayyar Afirka ta dauki matakin shigar da HKI cikin kungiyar ba tare da shawartar sauran kasashen kungiyar ba.

Ministan ya kara da cewa a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, zai kai ziyarar aiki zuwa wasu kasashen Afirka don tattauna wannan batun, don kuma samun goyon bayan tabbatar da kasar Falasdinu mai cikekken ‘yanci.

Labarin ya kara da cewa sauran kasashen Afirka da suka nuna goyon bayansu ga wannan bukata ta korar Isra’ila a matsayin mamba mai sanya ido a kungiyar AU dai, sun hada da Afirka ta Kudu, Tunisiya, Eriteriya,Senegal, Tanzaniya, Nijar, Najeriya, Gabon, Zimbabwe, Laberiya, Tsibirin Comoros da kuma Sychelle.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!