Tataccen Sanadarin “Uranium” Da Iran Take Ajiya Ya Kai Kilo 55

2021-04-07 14:46:28
Tataccen Sanadarin “Uranium” Da Iran Take Ajiya Ya Kai Kilo 55

Kakakin hukumar makamashin Nukiliya ta Iran ne ya bayyana cewa; Sanadrin na Uranium din da aka tace bisa darajar da ta kai 20%, da ake ajiye da shi ya kai kilogiram 55.

Kakakin hukumar makamashin Nukiliyar ta Iran Behruz Kamalvandi ya ci gaba da cewa; “ Wani abu mai muhimmanci shi ne yadda sabuwar dokar majalisar shawarar musulunci ta Iran ta samar da daidaito a cikin yarjejeniyar ta Nukiliya, yana mai kara da cewa; Wani bangare da wannan dokar shi ne samar da tataccen “Uranium” da ya kai daraja 20% yawansa zai kai kilo 120 a kowace shekara.

Behruz Kamalvandi ya kuma ce; Ya zuwa yanzu ana da kilo 55, da hakan yake nuni da cewa za mu iya cimma wancan adadin a cikin kasa da watanni takwas.

Wannan sanarwar dai ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa a tsakanin Iran da kasashen da suke cikin yarjejeniyar a birnin Vienna na kasar Austria.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!