Shugaban Kasar Nijar Muhammad Bazoum Ya Kira Yi Kasashe Da Su Yi Aiki Da Nauyin Da Ya Rataya A Wuyansu Dangane Da Kare Muhalli

2021-04-07 14:43:11
Shugaban Kasar Nijar Muhammad Bazoum Ya Kira Yi Kasashe Da Su Yi Aiki Da Nauyin Da Ya Rataya A Wuyansu Dangane Da Kare Muhalli

Shugaban kasar ta Nijar wanda ya gabatar da jawabi ga kwamiti mai kula da muhalli da kuma matsalar cutar corona ta hanyar bidiyo daga nesa ya kira yi kasashe da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu a karkashin yarjejeniyar Paris ta kare muhalli.

Shugaba Muhammad Bazoum a cikin jawabin nasa ya bayyana cewa; Cutar Covid-19 da kuma kalubalen sauyin muhalli sun zo a wani lokaci a tare, inda su ka ci dunun kasashen da suke fama da matsaloli.

Shugaban kasar na jamhuriyar Nijar ya kuma ce: “ A nahiyar Afirka, ba ya ga fada da ake yi da cutar corona, da akwai kuma wata kokawar ta fuskantar sauyin yanayi.”

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!