Fara Yi wa Mutane Rigakafin Corona A Jihoji 8 Na Sudan

2021-04-07 14:39:38
Fara Yi wa Mutane Rigakafin Corona A Jihoji 8 Na Sudan

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Sudan ta sanar da cewa; Daga ranar Lahadi mai zuwa 11 ga watan nan na Aprilu, za a fara yin allurar rigakafin cutar corona a cikin jihohi 8 na kasar. Jihohin dai sun hada da Nahru-Nil, al-shumaliyyah, al-bahrul-ahmar, shumal-Kurdufan, Garb-kurdufan, junub Kurdufan, shumal kurdufan.

Sanarwar ta kuma ci gaba a cewa; Tuni an fara bayar da horo ga ma’aikatan kiwon lafiya akan yadda za su yi wa mutane allurar ba tare da wata matsala ba.

Tun da fari dai ma’aikatar kiwon lafiyar kasar ta Sudan ta bayyana cewa; “ Tun a ranar 28 ga watan Maris ne aka fara yi wa ma’aikatan kiwon lafiya da mutanen da suka manyanta allurar rikagafin ta cutar corona, kuma adadinsu ya kai 58,072.”

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!