Ministan Harkokin Wajen Kasar Iraki Ya Bukaci A Maida Kasar Siriya Cikin Kungiyar Kasashen Larabawa

2021-02-24 08:52:59
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iraki Ya Bukaci A Maida Kasar Siriya Cikin Kungiyar Kasashen Larabawa

Ministan harkokin wajen kasar Iraki Fu’ad Husain ya bayyana muhimmancin maida kasar Siriya cikin kungiyar kasashen Larabawa.

Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya nakalto Husain yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda yake ganawa da Naif Al-Hajraf sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin Tekun Farisa a birnin Riyad na kasar Saudiya.

Ministan ya kara da cewa, zaman lafiya a kasar Iraki ya na da tasiri a kan kasashen yankin Tekun farisa, don haka ya bukaci aiki tare tsakanin kasashen yankin don dawo da zaman lafia a kasar ta Iraki.

A nashi bangaren Al-Hajraf ya bayyana goyon bayansa ga kungiyar kasashen Laraba na yankin tekun Farisa, da kuma goyon baya ga kokarin dawo da zaman lafiya a yankin daga ciki har da kasar Iraki.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!