Nijar : Mohammed Bazoum, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Da Kashi 55,75 %

2021-02-23 22:07:34
Nijar : Mohammed Bazoum, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Da Kashi 55,75 %

Dan takaran jam’iyya mai mulki a jamhuriyar Nijar, cewa da Bazoum Mohammed, ya lashe zaben shugabancin kasar a zagaye na biyu da kashi 55,75 cikin dari na yawan kuri’un da aka kada, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.

Sakamakon wucin gadi da hukumar ta CENI ta sanar da yammacin yau Talata, dan takara jam’iyyar adawa ta RDR-Canji, Mahamane Usman, ya samu kashi 44,25 cikin dari na yawan kurin zaben zagaye na biyu da aka kada kuri’arsa a ranar Lahadi data gabata.

Saidai tun kafin bayyana sakamakon, gamayar jam’iyyun adawa na kasar suka fitar da sanarwar watsi da sakamakon, tare da gargadin hukumar da kada ta sanar da sakamakon mai cike da magudi.

Rahotanni daga kasar sun ce tuni magoya bayan jam’iyyun adawa sunka fantsama kan tituna inda sukayi ta kone konen tayoyi a Yamai babban birnin kasar.

Yanzu dai hukumar zaben kasar za ta mika wannan sakamakon ga kotun tsarin mulkin kasar domin neman amincewa.

Idan kotun tsarin mulkin ta amince da sakamakon Mohammed bazoum, zai sama shugaban kasar na biyu a karkashin jamhuriya ta bakwai, inda zai gaji shugaban kasar mai baring ado Alhaji Mahammadu Issoufou, wanda wa’adinsa ke kawo karshe.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!