Iran Ta Kawo Karshen Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da IAEA

2021-02-23 22:05:06
Iran Ta Kawo Karshen Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da IAEA

Iran, ta sanar a wannan Talata da kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna ta tsakaninta da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, kamar yadda majalisar dokokin kasar ta bukata, idan dai har Amurka ba ta dage wa kasar takunkumi ba zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.

Yarjejeniyar dai na baiwa hukumar ta IAEA, damar gudanar da ziyarar ba zata a tashohin nukiliyar kasar ta Iran.

Haka kuma Iran, ta sanar da katse na’urorin kyamera na hukumar a tashohin nukiliyarta, sannan kuma ba zata taba baiwa hukumar faya fayan bidiyo dake tashohin ba kamar yadda aka saba a baya, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya sanar wa manema lanarai.

Saidai Muhamad Jawwad Zarif, ya ce duk da hakan Iran za ta ci gaba da hulda da hukumar, kamar yadda yarjejeniyar hana yaduwar makamman nukiliya ta duniya ta tanada.

M. Zarif, ya kuma Iran, ba za ta shiga wata tattaunawa a hukumance da Amurka ba, a matsayinta na wacce ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!