An Fara Yi Wa Jama’a Allurar Riga Kafin Korona A Senegal

2021-02-23 21:59:33
An Fara Yi Wa Jama’a Allurar Riga Kafin Korona A Senegal

Senegal, ta kaddamar da yiwa jama’arta allurar riga kafin cutar korona, da allurar kamfanin harhada magunguna na kasar China Sinopharm.

An kaddamar yin riga kafin ne da hukumomin kasar a wani mataki na shawo kan al’umma su amince da sahihancin maganin.

Ministan kiwon lafiya na kasar ne aka fara yi wa riga kafin, kafin daga bisani a yi wa wasu manyan jami’an kasar, ciki har da ministar harkokin waje.

Za’a dai yi wa masu shekaru sama da 60 da kuma jami’an kiwon lafiya riga kafin.

Senegal dai ta ce ba zata jira, maganin da aka tanadar baiwa kasashe a cikin tsarin na nan Covax.

Kan hakan kasar ta yo ador riga kafin 200,000 daga kasar China, kuma nan gaba zata cimma yarjejeniyar sayan wani daga kasar Rasha.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!