​Tanzania: Magufuli Ya Amince A Dauki Matakai Domin Kariya Daga Cutar Covid-19

2021-02-23 21:38:31
​Tanzania: Magufuli Ya Amince A Dauki Matakai Domin Kariya Daga Cutar Covid-19

Shugaban kasar Tanzania Jhon Magufuli, ya kirayi al’ummar kasar da su rika daukar matakan kariya daga kamuwa da cutar corona.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, Shugaban kasar Tanzania Jhon Magufuli, ya yi wani jawabi ga al’ummar kasar, wanda a cikinsa ya nuna amincewarsa da samuwar cutar corona a kasar.

Magufuli, a baya ya bayyana cutar corona da cewa ba komai ba ne illa ayyukan Shaidan, da kuma ayyukan sabo da mutane suke aikatawa, saboda haka musulmi da kirista su dukufa wajen addu’a, ta hanyar haka ne kawai za a iya kawo karshen wannan matsala.

Haka nan kuma ya nuna shakku kan ingancin allurar rigakafin da kasashen turai suka samar, inda ya ce idan har za su iya samar da allurar rigafin wanann cuta cikin kan kanin lokaci, me yasa ba su samar da rigakafin malaria da kuma kanjamau ba.

A cikin ‘yan kwanakin na wasu daga manyan jami’an gwamnatin kasar Tanzania sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar corona, wanda hakan yasa shugaba Magufuli ya kirayi jama’a da su kara inganta matakan kariya, da kuma kiyaye tazara gami da saka takunkumin fuska, da kuma kula da tsafta.

Matakin da Magufuli ya dauka kan wannan batu dai ya fuskanci martani daga kasashen turai da kafofin yada labaransu.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!