Masar:Kamfanin Jiragen Sama Na “Egypt Air” Ya Dakatar Da Tashin Jiragensa Samfurin Boeing 777-200 Guda 4

2021-02-23 12:28:13
Masar:Kamfanin Jiragen Sama Na “Egypt Air” Ya Dakatar Da Tashin Jiragensa Samfurin Boeing 777-200 Guda 4

Jaridar ‘Egypt Today’ ta kasar Masar ta nakalto majiyar kamfanin jirage sama na kasar wato EgyptAir ta na cewa kamfanin ya dakatar da tashin jiragen saman kamfanin guda 4 samfurin Boeing 777-200 , saboda bukatar kanfanin kera jirage na Boeing, na a dakatar tashin irin wadannan jirage. Boenge ta daki wannan matakin ne sobota konewar da ingin jirgi mai kama da su da aka samu a Jihar Calorado na kasar Amurka.

Jaridar ta kara da cewa, injin jirgin na hannun dama, mallakin kamfanin jiragen sama na ‘United Airline’, ya kama da wuta jim kadan baya tashinsa, kuma har wasu sassa na injin din sun yi ta faduwa a kan gidajen mutane a yankin. Sai dai Jirgin ya sake komawa inda ya tashi tare da amfani da inji guda, ya kuma sauka lafiya ba tare da fasinjoji 231 da kuma ma’aikata 10 da suke cikin jirgin sun sami ko kwarzane ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!