Gwamnatin Sin Ta Bukaci Amurka Ta Koma Cikin Yarjejeniyar JCPOA Ta Kuma Dagewa Iran Takunkuman Tattalin Arziki

2021-02-23 12:20:14
Gwamnatin Sin Ta Bukaci Amurka Ta Koma Cikin Yarjejeniyar JCPOA Ta Kuma Dagewa Iran Takunkuman Tattalin Arziki

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira gwamnatin shugaban Biden ta koma cikin yarjejeniyar JCPOA na shirin nukliyar kasar Iran, ta kuma dage takunkuman da gwamnatin da ta shude ta dorawa kasar, a matsayin hanya tilo na kawo karshen halin tababan da ake ciki a yankin tsakanin Iran da Amurka.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakkin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Sin, Wang Wenbin ya na fadar haka a jiya Litinin. Ya kuma yi kira ga bangarorin biyu kan su daina yin wani abu wanda zai hana samun fahintar juna tsakanin kasashen biyu.

Daga karshe Wang ya yi maraba da yarjejeniyar fahintar juna tsakanin hukumar IAEA da Iran na tsawaita takaitaccen sanya ido na hukumar a ayukan nukliyar kasar ta Iran na tsawon watanni uku.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!