Siriya:’Yan Ta’adda Sun Hana Mutanen Idlib Kai Kawo A Wata Mashiga A Arewacin Lardin

2021-02-23 12:08:33
Siriya:’Yan Ta’adda Sun Hana Mutanen Idlib Kai Kawo A Wata Mashiga A Arewacin Lardin

Labaran da suke fitowa daga arewacin kasar Suriya sun bayyana cewa ‘yan ta’adda na kungiyar 'Kasad' sun rufe wata mashiga a yankin Idlib wanda sojojin kasar suka bude a jiya litinin.

Tashar talabijin ta Rusiyal Yau ta bayyana cewa sojojin kasar siriya a yankin sun bude mashigar Attarnabah daga arewacin lardin ne don bawa mutanen yankin damar ficewa karakashin ikon Kasad masu samun goyon bayan Amurka, ko kuma don samun bukatun yau da kullum.

Labarin ya kara da cewa yan ta’adda na kungiyar Kasad suna amfani da fararen hula na lardin Idlib a matsayin garkuwa don haka sojojin gwamnatin kasar kai masu hare-hare.

Muhammad Tanuf gwamnan lardin na Idalin ya fadawa Rusiyal Yaum kan cewa sun bude mashigar Attarnabah ne don ganin mutanen lardin sun koma yankunan da suke karkashin ikon sojojin gwamnatin kasar. Banda haka suna amfani da mashiga don kai kayakin agaji ga mutanen lardin, wadanda suka hada da na kiwon lafiya, abicni da sauransu. Rufe mashigar ba karamin asara ce ga mutanen lardin ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!