Musulmin Uyghur Na Kokawa Kan Matakan Da Gwamnatin China Take Dauka Domin Takura Su
2021-02-23 08:25:45

Shugaban gayammar kungiyoyin musulmin kabilar Uyghur Isa Dulkun, wanda kuma dan siyasa ne mai wakiltar yankinsa a kasar China, ya bayyana cewa, ko shakka babu a cikin shekarun baya-bayan nan gwamnatin kasar tana daukar matakai na takura wa musulmin Uyghur na kasar da sunan yaki da tsatsauran ra’ayi, wanda hakan ba gaskiya ba ne.
Isa Dulkun wanda aka Haifa a yankin Xinjiang, wanda mafi yawan mazaunan
yankin musulmi ne ‘yan kabilar Uyghur, ya bayyana cewa, daukar matakan nuna
musu wariya da mahukuntan China suke yi ba sabon lamari ba ne, amma dai a cikin
shekarun baya-bayan nan lamarin yafi tsananta, sakamakon daukar matakai da ake
na hana su gudanar da harkokinsu na addini, bisa wasu hujjoji marasa tushe.
Haka nan kuma ya yi ishara da cewa,
ana kiransu da kabilar marasa rinjaye a kasar China, ya ce su ba marasa rinjaye
ba ne, domin kuwa su ‘yan kasar China ne kamar kowa, suna da hakki kamar kowane
mutum a kasar a matsayinsa na dan kasa, to amma dukkanin matsalolin da
suke fuskanta da banbancin da ake nuna musu, hakan na faruwa ne saboda su
musulmi ne.
031
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!