An Kai Hari Akan Yankin Da Muhimman Cibiyoyin Gwamnati Su Ke A Birnin Bagadaza
2021-02-23 08:12:47

Majiyar tsaron Iraki ta ce an harba makaman roka akan yankin da ake kira; “Green Zone” da ke tsakiyar birnin Bagadaza, wanda yake kunshe da muhimmanc cibiyoyin gwamnati da ofisoshin jakadancin waje.
Sai dai majiyar tsaron ta ce harin
bai yi sanadiyyar asarar rayuka ko jikkatar wani mutum ba.
Tun da fari an ji karar jiniya a
yankin bayan da wani makami mai linzami samfurin “Katusha” ya fadi a yankin.
Daga lokaci zuwa lokaci ana harba makamai
masu linzami a yankin, wanda a wasu lokuta yakan lalata wasu gine-gine.
Ba kuma kasafai akan sami wasu
daukar nauyin kai harin ba.
031
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!