​An Fara Yin Kira Da Sake Bincike Kan Yadda Aka Kashe Malcolm X

2021-02-22 21:16:59
​An Fara Yin Kira Da Sake Bincike Kan Yadda Aka Kashe Malcolm X

Dangi da iyalan fitaccen dan gwagwarmayar kare hakkokin bakaken fata a kasar Amurka Malcolm X sun bukaci da a sake dawo da batun bincike kan musabbabin kisansa.

Yayin gudanar da wani taron manema labarai a jiya a taron tunawa da cikar shekaru 55 da kisan mahaifinta, diyar Malcolm X Ilyasa Al-shabbaz ta bayyana cewa, a matsayinsu an iyalansa, suna bukatar a sake dawo da batun bincike kan kisan gillar da aka yi masa.

Wannan na zuwa dai bayan samun wasu bayanai da ke nuni da cewa, akwai hannun jami’an ‘yan sanda na birnin New York da kuma na hukumar tsaro ta FBI wajen kisan Malcolm X.

Shekaru hamsin da biyar da suka gabata a ranar 21 Febrairu shekara ta 1965, wasu mutane uku suka bude wutar bindiga a kan Malcolm X, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a Audubon a cikin New York.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!