Daga Gobe Talata, Iran Ba Za Ta Sake Barin Masu Sa-Ido Su Ziyarci Cibiyoyinta Na Nukiliya Ba

2021-02-22 13:37:24
 Daga Gobe Talata, Iran Ba Za Ta Sake Barin Masu Sa-Ido Su Ziyarci Cibiyoyinta Na Nukiliya Ba

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf, ya bayyana cewa; aiki da tsarin sanya idon na ba zata, zai tsaya baki daya daga gobe Talata 23 ga watan nan na Febrairu.

Muhammad Baqir Qalibaf ya rubuta haka ne a shafinsa na Twitter a yau Litinin, inda ya ce; Bisa dokar da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi, daga gobe Talata, aiki da tsarin na kai ziyara da masu sa-ido na hukumar makamashin Nukiliya su ke yi, zai tsaya baki daya, ba kuma za a sake barinsu zuwa cibiyoyin Nukiliyar ta Iran ba.

Qalibaf ya ce; Aiwatar da tsarin aiki tare tsakanin Iran din da hukumar zai kasance ne a karkashin doka ta 9 ta yarjejeniyar da take nufin aiki da ita ba tare da kari ba.

031

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!