Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kai Hari Akan Birnin Ma’arib Na Kasar Yemen

2021-02-22 13:35:29
 Jiragen Yakin Saudiyya Sun Kai Hari Akan Birnin Ma’arib Na Kasar Yemen

Jiragen Yakin na Saudiyya sun kai munanan hare-hare a garin na marib ne adaidai lokacin da sojojin halartacciyar gwamnatin kasar ta San’aa suke gaba da kwace iko da shi.

Manufar hare-haren na Saudiyya dai shi ne hana sojojin na Yemen karbe iko da birnin, sai dai wasu rahotanni suna nuni da cewa sojojin suna nausawa ta kusurwowi mabanbanta.

Tuni dai sojojin Yemen din su ka kwace iko da yankin Raghawan dake yammacin birnin na Ma’arib.

A halin da ake ciki a yanzu saudiyya tana fuskantar matsin lamba mai tsanani domin kawo karshen yakin da take yi da kasar Yemen.

Tun a 2015 ne dai Saudiyya ta kafa kawancen yaki da Yemen, wanda ya zuwa yanzu ya ci dubban rayukan mutane da kuma jikkata wasu dubbai.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!