Shugaban Kasar Nijar Muhammadu Issufu Ya Bayyana Cewa; Zaman Lafiya Mai Dorewa Da Aka Rasa A Kasar Zai Sake Dawowa

2021-02-22 13:32:09
 Shugaban Kasar Nijar Muhammadu Issufu Ya Bayyana Cewa; Zaman Lafiya Mai Dorewa Da Aka Rasa A Kasar Zai Sake Dawowa

Shugaban kasar ta Nijar, wanda ya kada kuri’arsa a zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka yi a jiya Lahadi, ya ci gaba da cewa; Kasar Nijar tana fuskantar kalubale na tsaro, haka nan na tattalin arziki da kiwon lafiya da kuma ci gaba.

Shugaba Muhammadu Issufo ya kuma ce; Muna da bukatar tsarin demokradiyya mai karko domin fuskantar wadannan kalubalen da suke a gabanmu.

Har ila yau, shugaba Muhammad Issufu ya kuma bayyana jin dadinsa da alfaharin cewa shi ne zaben shugaban kasar farko da aka zaba ta hanyar demokradiyya a kasar ta Nijar.

A jiya Lahdi ne dai aka yi zaben shugaban kasa zagaye na biyu a tsakanin Muhammadu Bazum da kuma Muhammad Usmmanu.

A gefe daya, mutane 7 ne su ka rasa rayukansu a wani harin ta’addanci da aka kai a yankin Tillaberi dake jamhuriyar ta Nijar a lokacin zaben shugaban kasa zagaye na biyu.

Kamfanin dillancin labarun AFP ya nakalto cewa; Dukkanin wadanda su ka rasa rayukan nasu ma’aikatan hukumar zabe ne ta kasar, yayin da wasu uku su ka jikkata.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!