Mutum Daya Ya Rasa Ransa Sanadiyyar Fashewar Wani Bom A Garin Dar’a Na Kasar Syria

2021-02-22 13:29:26
Mutum Daya Ya Rasa Ransa Sanadiyyar Fashewar Wani Bom A Garin Dar’a Na Kasar Syria

Bom din da ya fashe yana daga cikin wanda ‘yan ta’adda su ka bari a wani gini da ke kauyen Aqraba da Arewacin Dar’a.

Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya amabto majiyar tsaro daga kasar Syria na cewa,bom din da ya tashi ya yi sanadiyyar mutuwar wani matashi makiyayi da ya fito daga kauyen Kafar-Nasij.

Gabanin janyewar kungiyoyin ‘yan ta’adda daga yankin sun dasa bama-bamai a cikin gidaje da gonaki da kuma muhimman cibiyoyin gwamnati.

Kasar Syria ta yi fama da hare-haren ‘yan ta’adda tun daga 2011, sai dai ta sami galaba akansu.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!