Iran Ta Sake Aikewa Da Jirgin Ruwa Mai Dauke Da Makamashi Zuwa Kasar Venezuela

2021-02-22 10:01:21
Iran Ta Sake Aikewa Da Jirgin Ruwa Mai Dauke Da Makamashi Zuwa Kasar Venezuela

Cibiyar da take bibiyar kai da komowar jiragen ruwa a duniya ta sanar a shafinta na “Twitter” kan cewa, Iran ta sake aikewa da jirgin ruwa dauke da makamashi zuwa kasar Venezuela.

Sanarwar ta kunshi cewa; Man da Iran din ta aike zuwa yankin El-Palito da ke kasar Venezuela, ya kai lita miliya 44, wanda shi ne karo na uku da Iran take aika makamashi zuwa Venezuela ta jiragen ruwa masu daukar makamashi.

A ranar 24 ga watan Mayu na 2020 ne dai Iran din ta fara aika man fetur zuwa kasar Venezuela a karkashin rakiyar jiragen ruwa na yaki na kasar ta Venezuela.

Jirgin ruwa na biyu dauke da makamashi na Iran zuwa kasar ta Venezuela ya isa kasar ne a ranar 25 ga watan Mayu na 2020.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!