An Sanar Da Mutuwar Mutane Fiye Da 200 Saboda Corona A Kasar Italiya

2021-02-22 09:51:02
An Sanar Da Mutuwar Mutane Fiye Da 200 Saboda Corona A Kasar Italiya

Ma’aikatar lafiya ta kasar Italiya ta sanar da cewa a cikin kwana daya rak, cutar ta corona da ta sake dawowa, ta ci rarukan mutane 232, yayinda adadin wadanda su ka kamu da ita kuwa suka kai 13,452.

Har ila yau sanarwar ta kara da cewa, ya zuwa yanzu dai, jimillar wadanda su ka kamu da cutar ta corona, sun kai 2,809,246, sannan wadanda su ka mutu kuwa sun kai 95,718. Kasar Italiya dai tana daga cikin kasashen turai wadanda cutar ta covid-19 ta fi yi wa illa, da ma duniya baki daya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!