Hukumar Wasan Kwallo Kafa Ta Duniya ( FIFA) Ta Kaddamar Da Makarantar Koyar Da Wasanni A Kasar Demokradiyyar Congo

2021-02-22 09:09:46
Hukumar Wasan Kwallo Kafa Ta Duniya ( FIFA) Ta Kaddamar Da Makarantar Koyar Da Wasanni A Kasar Demokradiyyar Congo

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino ya kaddamar da aikin ginawa da kafa makarantar bayar da horon kwallon kafa, tare da shugaban kasar Demokradiyyar Congo, Felix Tsetsekedi na democradiyyar Congo wanda kuma shi ne shugaban riko na tarayyar Afrika.

Infantino ya bayyana cewa;

"Mun kaddamar da makarantar a nan kasar Demokrdiyyar Congo, wacce kuma za ta kafa kwatankwacinta a fadin nahiyar Afirka, domin wajibi ne karatu da kwallon kafa su tafi kafada da kafada.”
A nashi bangaren, ministan wasannin kasar ta Congo Amos Mbayo , ya ce, "dama Muna da matsalolin da muke fuskanta, ta fuskar wasanni, amma ga shi FIFA ta ba mu dama, domin samar da ‘yan wasa masu kuzari. Don haka zamu yi kokari mu yi amfani da wannan damar.”
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!