Australian Open: Djokovic Ya Lashe Gasar Tennis Na 9TH A Australia
2021-02-22 08:58:53

Novak Djokovic ya lashe wasan Tennis na 9Th wanda ake kira 'Autralian Open' bayan da ya lallasa tokwaransa na kasar Rasha Daniil Medbedev har sau ukku.
A zagaye na farko na wasan an tashi 7-5 a na biyu kuma aka tashi 6-2 sai kuma zagaye na ukku wanda aka tashi shi ma 6-2.
Djokovic dai bai taba rasa wasa ta karshe da ya saba shiga ba, sannan a wannan wasan ya dauki kofin ne bayan ya dauki awa daya da minti 53 yana fafatawa da Medbedev.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!