Tattaunawa Ta Yi Zafi Tsakanin Iran Da Hukumar IAEA

2021-02-21 21:34:02
Tattaunawa Ta Yi Zafi Tsakanin Iran Da Hukumar IAEA

Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya, IAEA, na ci gaba da tattaunawa da hukumomin Tehran.

Da yammacin yau Raphael Grossi, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif.

Ziyarar ta Mista Grossi, na zuwa ne a yayin da Iran ta sanar da yiyuwar hana hukumar sanya ido kan shirin nukiliyar kasar ta Iran.

Bayanai sun ce tattaunawar bangarorin biyu ta yi zafi sosai, inda nan gaba ake sa ran zasu fitar da wata sanarwa.

jiya Asabar, shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, ya fara ziyara a birnin Tehran, a wani mataki na shawo kan hukumomin kasar akan kada su dau matakin hana hukumar gudanar da ayyukan sanya ido shirin nukiliyar kasar ta Iran.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!