An Bankado Yadda Isra’ila Ta Yi Musayar Fursunoni Da Siriya

2021-02-21 21:32:01
An Bankado Yadda Isra’ila Ta Yi Musayar Fursunoni Da Siriya

Kafofin yada labarai, sun bankado wata musayar fursunoni ta tsakanin Isra’ila da Siriya.

An yi musayar ce da wata ‘yar Isra’ila data tsallaka Siriya bisa rajin kanta da kuma wasu makiyaya biyu wadanda bisa ga dukan alamu su kuma ‘yan Siriyar ne.

Isra’ilar, ta kuma rage wa’adin zama gidan yari ga wasu fursunoni biyu.

An dai yi musayar ce a shiga tsakanin kasar Rasha, a cewar rahotannin.

Jaridar Haaretz ta Isra’ila, wacce ta yi kaurin suna wajen adawa da manufofin gwmanatin Netanyahu, ta yi babban labarinda da aza ayar tambaya kan yadda lamarin ya faru, wanda ta danganda da siyasa, a daidai lokacin da ya rage wata guda a je zabe.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!