Iran Tana Nazarin Gayyatar Tarayyar Turai Na Hallatar Taron JCPOA Wanda Wakilin Amurka Zai Halarta
2021-02-21 15:03:32

Matimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi
ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran tana nazarin gayyatar tarayyar Turai don
halattan taron kasashe P4+1 wadanda suka samar da yarjejeniyar shirin nukliyar
kasar wacce aka fi sani da JCPOA daga cikin har da wakilin kasar Amurka.
Ariqchi ya kara da cewa Iran zata yi nazarin wannan bukatar
tare da sauran kawayenta wadanda suka hada da Rasha da kuma Sin. Ana saran idan
Iran Iran ta amince da halattan taron gwamnatin shugaban Biden na Amurka zai
tura Rob Malley mai bashi shawara na musamma
kan al’amuran kasar Iran zuwa Taron.
Amurka ta fice daga yarjejeniyar JCPOA a shekara ta 2018
sannan ta take dukkan dokokin kasa da kasa kan yarjejeniyar nukliyar kasar
Iran, ta dora mata takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasar.
Josep Borrell jami’ii mai kula da lamuran kasashen waje na tarayyar Turai ne ya gabatar da wannan bukatar a ziyarar da yake yi a nan birnin Tehran.
Tags:
kasashe p4+1
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!