Rasha:'Yan Ta’adda A Lardin Idlib Na Kasar Siriya Suna Shirin Kai Hari Da Makaman A Yankin Don Dorawa Gwamnatin Kasar Laifi

2021-02-21 14:37:09
Rasha:'Yan Ta’adda A Lardin Idlib Na Kasar Siriya Suna Shirin Kai Hari Da Makaman A Yankin Don Dorawa Gwamnatin Kasar Laifi

Gwamnatin kasar Rasha ta bada sanarwan cewa kungiyar ‘yan ta’adda ta Tahrirul Sham da ke a yankin Idlib na kasar Siriya ta na shirin watsa makaman guba a yankin, da nufin dora laifin yin haka kan gwamnatin kasar.

Cibiyar sasanta bangarorin da suke sabani a kasar Siriya ta kasar Rasha, ta bayyana haka ne a jiya Asabar. Cibiyar ta kuma kara da cewa tuni ta sami labarin cewa kungiyar ta kai wata mota makare da sindaran guba a garin Tarmanin, don watsa shi a cikin fafaren hula a yankin nan gaba da wannan manufar.

Kasar Rasha, har’ila yau ta na zargin hukumar yake da amfani da makaman guba a duniya (OPCM) da nuna wariya a a cikin ayyukanta.

Rear Admiral Vyacheslav Sytnik, mataimakin shugaban cibiyar sasanta mutanen kasar Siriya ya bayyana cewa kungiyar “white Helmet’ ta na aiki da ‘yan ta’addan don dora laifi amfani da makaman na guba kan kan gwamnatin kasar ta Siriya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!