Gasar Spanish La Liga:Real Madrid Da Valladolid Sun Tashi 1-0

2021-02-21 14:15:29
Gasar Spanish La Liga:Real Madrid Da Valladolid Sun Tashi 1-0

A ci gaba da gasar Spanish La Liga, a jiya kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lallasa Valladolid wanda ya bata damar sake dawowa kan matsayi na biyu.

‘Yan kungiyar Zinedine Zidane dai sun jinkirta har zuwa minti na 65 da fara wasan kafin su saka kwallo tilo wanda ya basu nasara a ragar Valladolid.

A wannan wasan dai kungiyar Real ta sami abinda take so don ta rage rattan da ke tsakaninta da kungiyar da take gaba da ita zuwa maki 3 kacal.

Har yanzun dai kungiyar kwallon kafa ta Atletico wacce take gaba a gasar ta Spanich La Ligo ta na da wani wasa a gaba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!